Mai Magana da yawun hukumar jiragen saman kasar FAAN Yakubu Dati, ya fada cikin wata sanarwa wadda ta iske kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, tuni kasar ta baza wasu nau'in karnuka tare da hadin gwiwar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a filayen jiragen saman kasar domin gudanar da bincike na musamman.
Najeriyar ta ce ba zata yi kasa a gwiwa ba, game da sha'anin tsaron filayen jiragen saman kasar, musamman kasancewar ana daf da gudanar da bukukuwan Easter.
Dati, ya kara da cewar, dama an sanya na'urorin dake daukar hotuna na shigi da fici a filayen jiragen saman kasar.
Sannan ya shawarci matafiya dasu tabbatar sun isa filayen jiragen a kan lokaci domin binkasarsu, don gudun kada suyi hasarar tikitin jiragensu.
An dai kaddamar da harin ne a filin jirgin sama na Zaventeen, da kuma tashar jiragen karkashin kasa a birnin Brussel na kasar Belgium da safiyar ranar Talatar data gabata, lamarin da yayi sanadiyyar hallaka mutane sama da 30. Kungiyar IS, tayi ikirarin kaddamar da harin.(Ahmad)