Cikin wata sanarwa da ya fitar, kanar Usman ya ce cikin kwanaki 12 sojojin sun fatattaki mayakan kungiyar a sansanonin su dake sassan wannan daji. A cewar sa dakarun tawagar ta 7 dake karkashin runduna ta 21 ta sojin kasar, sun hallaka 'yan ta'adda da dama, sun kuma kori 'yan kungiyar daga kauyuka 4 da kuma wasu wuraren da suke samun mafaka a yankunan Bala Karege, da Goske, da Harda da kuma Markas 3.
Sanarwar ta kara da cewa ya zuwa ranar Lahadi 8 ga watan Mayun nan, sojojin sun shiga wadannan sassa, inda a wurare da dama 'yan Boko Haram din sun riga sun arce kafin shigar sojojin.
Kaza lika sanarwar ta ce dakarun sojin sun gano makamai da sauran kayan fada da mayakan na Boko Haram ke amfani da su. Har wa yau a cewar kanar Usman, mayakan kungiyar sun yi amfani da ruwan sama mai karfi da aka tashi da shi a ranar Lahadi, wajen matsawa sansanin sojojin Najeriyar dake dajin na Sambisa. (Saminu)