Kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ya bukaci ofishin jakadancin Amurka dake birnin Pretoria, da ya yi bayani game da zancen babban jami'in jam'iyyar ANC mai rike da ragamar mulkin kasar Afirka ta Kudu, cewar Amurka tana yunkurin tube jam'iyyar daga karagar mulki.
A nasa bangare, kakakin jam'iyyar ANC Zizi Kodwa ya shedawa wakilin Xinhua cewar, an sanya wasu daliban kasar Afirka ta Kudun dake karatu a Amurkar da su yi leken asiri dangane da yunkurin canza gwamnatin kasar Afirka ta Kudu.
Dangane da zargin da aka yi wa gwamnatinta, Cynthia Harvey, kakakin ofishin jakadancin Amurka a Afirka ta Kudu, ba ta ce uffan ba game da amincewa ko karyata zargin da ake yiwa Amurkar.
Ta ce akwai wasu dalibai 'yan Afirka ta Kudu 46 da suka halarci shirin horar da matasa 'yan Afirka na Mandela Washington Fellowship a shekarar 2014, amma ba ta san ainihin abubuwan da aka koyar da su a Amurka ba.(Bello Wang)