Rahotanni na cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ce, jagoran bangaren da ke adawa da gwamnatin Sudan ta Kudu, Riek Machar ya bayyana amincewa da nadin da shugaba Salva Kiir Mayardit ya yi masa na zama mataimakinsa na farko.
Game da wannan batu, Hong Lei ya ce, Sin tana maraba da ci gaban da aka samu a kokarin da ake yi na shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu. Tana kuma fatan za a hanzarta kafa gwamnatin hadaka da za ta kunshi dukkan al'ummomi, domin sa kaimi ga wannan yunkuri. Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa tare da sauran kasashe da kungiyoyin duniya da abin ya shafa, domin sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a kasar yadda ya kamata.(Fatima)