Hakan dai ya biyo bayan zargin da aka dade ana yi, cewa kotun na nunawa nahiyar Afirka banbanci cikin ayyukan ta, matakin da ya sabawa manufar kafa ta. Ministar wadda ta bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin wani taron manema labarai a birnin Pretoria, ta kara da cewa kasar ta, zata tattauna da daukacin masu ruwa da tsaki, tare da ita kanta kotun ta ICC, domin kara nazartar yanayin da ake ciki, kafin kaiwa ga daukar matakin karshe.
Kalaman na Nkoana-Mashabane dai tamkar jaddada ra'ayin da shugaba Jacob Zuma ya gabatar ne, yayin taron kungiyar AU da ya gabata a 'yan kwanaki, inda ya bayyana rashin gamsuwar kasar sa ga ayyukan ICCn, tare da bayyana yiwuwar janyewa daga goya mata baya.(Saminu Alhassan)