Kafofin watsa labaru na kasar Faransa sun tsamo maganar kakakin hukumar binciken tsaron jiragen saman kasar Faransa na cewa, bisa abubuwan da tsarin sadarwa da bada rahoto na jirgin saman MS804 ya sanar kafin ya daina aiki, an ce, akwai hayaki a cikin bayan gida dake wurin dab da dakin matukin jirgin saman. Kakakin ya kara da cewa, kafin a yi kokarin gano takarcen jirgin saman da bakin akwatin nadar bayanai, akwai wuya a tabbatar dalilin faduwar jirgin saman .
Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya jaddada a birnin Paris cewa, game da dalilin faduwar jirgin saman, yanzu kasar Faransa tana binciken dukkan hasashen da aka yi game da dalilin faduwar jirgin saman, amma ba ta nufin goyon bayan dukkan ko wane irin hasashe ba. Ya ce, yanzu aikin dake gaban kome shi ne neman jirgin saman, ciki har da neman bakin akwatin nadar bayanan jirgin saman da kuma yin bincike a kai. (Zainab)