in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya nuna juyayi ga faduwar jirgin sama na kasar Masar
2016-05-21 13:45:03 cri

Bangaren soja na kasar Masar ya sanar a jiya Jumma'a cewa, rukunin ceto ya samu tarkacen jirgin sama da ya fadi na kamfanin jiragen sama na kasar Masar a yankin teku dake da nisan kilomita 290 daga arewacin birnin Alexandria. A halin yanzu, bangarori daban daban ba su iya tabbatar da dalilin wannan hadarin ba. A wannan rana kuma, kakakin babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya ba da sanarwa, domin nuna juyayi game da wannan hadari, inda ya jajanta wa iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon hadari da kuma gwamnatocin da hadarin ya shafa.

A shekaran jiya, wato ranar 19 ga wata, wani jirgin sama na A320 na kamfanin zirga-zirgar jiragen saman kasar Masar wanda ya tashi daga birnin Paris na kasar Faransa zuwa Alkahira na kasar Masar ya bace a yankin tekun Bahar Rum, tare da fasinjoji 56, masu aikin tsaro 3 da kuma ma'aikatan jirgin saman 7.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China