Shugaba Xi ya ce kasar Sin sahihiyar abokiyar kasar Afghanistan ce duk da irin canje-canjen da ake fuskanta a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Don haka ya lashi takwabin hada kai da kasar Afghanistan don daukar matakan da suka dace na gina hanyar siliki na tattalin arziki, kuma kasar Sin na goyon bayan kamfanoninta da su zuba jari a Afghanistan.
A nasa bangaren Shugaba Karzai ya yaba da dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kasar Sin sahihiyar makwabciya ce. Afghanistnan ta yaba da irin goyon bayan da take bayar wa wajen sake gina kasar cikin lumana.
Shugaba Karzai ya zo Sin ne don halartar taron kolin tattaunawa kan inganta cudanya da karfafa hadin gwiwa a nahiyar Asiya da aka shirya gudanarwa a ranar Talata da Laraba a birnin Shanghai. (Ibrahim)