in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kira taron manyan hafsoshin sojin kasashen mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai
2014-08-29 10:48:24 cri

A kira taro karo na 3 na manyan hafsoshin sojin kasashen mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai a ranar alhamis 28 ga wata a nan birnin Beijing.

Mamban kwamitin da ke kula da harkokin soja na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma babban hafsan hafsoshin kasar Sin Fang Fenghui a cikin jawabin da ya gabatar ya ce bayan da aka shafe tsawon shekaru 13 ana raya ta, kungiyar hadin kai ta Shanghai, ta riga ta zama wani tsari mai amfani da wani rukuni mai muhimmanci wajen sa kaimi ga bunkasuwar mambobi, da kiyaye zaman lafiya a wannan shiyya har duk duniya baki daya.

Kasar Sin in ji shi ta gabatar da shawarwari guda hudu, da suka hada da tsayuwa tsayin daka kan ra'ayin kasar na amincewa da juna, da samun moriyar juna, da yin shawarwari da juna, da girmamawa al'adu daban daban, da samun bunkasuwa tare.

Ya ce shawara ta biyu shi ne a tsaya tsayin daka kan kafa wata shiyya da ke samun zaman lafiya cikin hadin gwiwa. Sannan na uku, a tabbatar da inganta amincewa da juna da hadin kai a fannin soji. Shawarar karshe kuma ita ce, tabbatar da ganin an kara hada kai wajen yaki da ta'addanci.

Mahalarta taron sun nuna gamsuwa ga kyakkyawan sakamakon da mambobin suka samu a hadin gwiwar harkokin tsaro da shimfida zaman lafiya, inda suka nuna cewa, suna son kara yin kokari domin zurfafa irin wanan hadi kan. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China