in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da musayar kasuwar hannayen jari ta Shanghai da ta Hongkong
2014-11-17 14:28:04 cri
Da misalin karfe 9 da rabi na safiyar Litinin din nan ne mamban hukumar harkokin siyasa, ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma sakataren kwamitin jam'iyyar na birnin Shanghai Hanzheng, da shugaban kungiyar sa ido kan kasuwar hannayen jari ta kasar Sin Xiao Gang, suka halarci bikin bude hada-hadar cinikayyar kasuwar hannayen jari ta birnin Shanghai.

Kaddamar da fara hada-hadar kasuwar ya shaida bude musayar hannayen jari a kasuwar Shanghai da ta Hongkong bisa sabon tsarin kasuwannin.

A kuma wannan rana, gwamnan yankin Hongkong Leung Chun-ying, da shugaban kungiyar kasuwar hannayen jari ta Hongkong Zhou Songgang, sun sanar da kaddamar da hada-hadar musayar kasuwar hannayen jarin ta Shanghai da Hongkong, a yayin zama da suka yi a babbar kasuwar hannayen jari ta Hongkong. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China