Rahotanni daga birnin na Shanghai dai na cewa baya ga wadanda suka rasa rayukansu, wasu mutanen 42 sun samu raunuka, yayin turmutsutsun da ya auku, lokacin da ake tsaka da shagulgula, a ranar jajibirin shiga sabuwar shekara.
Game da aukuwar wannan lamari, shugaba Xi ya umarci mahukuntan na Shanghai, da su tabbatar an baiwa wadanda suka jikkata kulawar da ta kamata. Kaza lika ya ce aukuwar lamarin darasi ne, dake nuna bukatar kulawa matuka, yayin da ake gudanar da bukukuwan gargajiya na al'adun Sinawa dake tafe nan gaba kadan.
Daga nan sai ya yi kira ga mahukunta, da jami'an tsaro, da su ci gaba da daukar matakan kare rayukan al'umma a ko da yaushe, musamman ma yayin bukukuwan da kan tara dubban jama'a wuri guda.
Shi ma a nasa tsokaci game da wannan batu, firaministan kasar Sin Li Keqiang, kira ya yi ga mahukunta a dukkanin matakai, da su kara kwazo wajen dakile dalilan dake haddasa hadarurruka da asarar rayuka.
Yanzu haka dai mahukuntan birnin na Shanghai sun bayyana kafa wata tawagar bada agaji, domin shawo kan tasirin wannan hadari. Yayin da kuma ake ci gaba da binciken musabbabin aukuwar sa. (Saminu Hassan)