A ran 7 ga watan Nuwamba, makarantar firamare ta koyon harsunan waje ta Jing'an dake Shanghai ta shirya bikin Kyakkyawar Afirka, ta yadda dalibanta za su iya kara sanin kasashen Afirka. Wannan biki ya kasance daya daga cikin bukukuwan "ratsa nahiyoyi biyar na duniya baki daya da kananan kafafu". An shirya wannan biki na kyakkyawar Afirka ne bisa fatan dukkan daliban makarantar za su iya zama masu son mutane, da kuma kasancewa wadanda za su iya daukar hakikanan matakan taimakawa yaran Afirka, da sauran mutanen da suke bukatar taimako.