An gudanar da aikin raya yankunan yin ciniki cikin 'yanci a birnin Shanghai lami lafiya
A ranar 27 ga wata, magajin birnin Shanghai Yang Xiong ya bayyana cewa, an gudanar da aikin gwajin yankunan yin cinikayya cikin 'yanci na birnin Shanghai da ke kasar Sin lami lafiya, daga ranar 8 zuwa ranar 23 ga watan Oktoba, mutane sama da dubu 30 sun je gudanar da aiki ko bayar da tambayoyi a wajen ofisoshinsu, ciki har da masu masana'antu da suka gudanar da ayyuka har sau 8421.
Ya zuwa yanzu, an amince da bankuna masu jarin waje na CITIBANK, da DBS, da HSBC da BEA da su kafa sassa a yankunan yin cinikayya cikin 'yanci, kuma ana ci gaba da la'akari da kafa sassansu a sauran bankunan a wurin.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, an kafa sabon tsarin gudanar da ayyuka a yankunan yin cinikayya cikin 'yanci, kuma nan gaba, za a ci gaba da daukar matakai wajen kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. (Bako)