in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da kare nau'o'in halittu
2016-05-23 10:56:24 cri
Jiya Lahadi ce ranar kare nau'o'in halittu ta duniya, a kuma wannan rana ne babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya gabatar da jawabi dake nuna cewa, a halin da ake ciki, ana ci gaba da fuskantar karewar wasu nau'o'in halittu iri daban daban a duniyar nan, don haka ya kamata mambobin MDD, da hukumomin majalissar, da al'ummomin kasa da kasa, da masana da kamfanoni da dai sauran bangarorin da abin ya shafa, su yi hadin gwiwar daukar matakai yadda ya kamata, domin karfafa ayyukan kiyaye nau'o'in halittu iri daban daban, ta yadda za a iya inganta dauwamammen ci gaban duniya baki daya.

Kaza lika Mr. Ban ya bukaci a ci gaba da amfani da albarkatun kasa yadda ya kamata, duba da muhimmancinsu ga al'umma wajen cimma wannan buri. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China