A yayin taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Mr. Steiner ya yi bayani kan wasu abubuwan da suka shafi babban taron da za a yi a birnin Nairobi. Ya ce, mahalartar taron za su tattauna batutuwan da suka shafi yadda ake fitar da gurbatacciyar iska, cinikin namun daji ba bisa doka ba, kare muhallin teku, tarin sharar kayan abinci, sharar masana'antu da dai sauransu.
A sa'i daya kuma, wakilan za su yi shawarwari kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Paris da aka cimma a karshen shekarar da ta gabata, da kuma neman dauwamammen ci gaban duniya. Haka kuma, ministocin dake kula da harkokin kiyaye muhalli sama da dari daya na kasashen duniya za su halarci tattaunawar da za a yi.
Taken taron na wannan karo shi ne" cimma burinmu na samun dauwamammen ci gaba a fannin kare muhalli bisa jadawalin samun dauwamammen ci gaba a shekarar 2030".Ana kuma sa ran za a tattauna sabbin batutuwan kare muhalli a yankuna da kuma a kasashe daban daban na duniya. Daga bisani kuma, za a zartas da wasu kudurorin da abin ya shafa, ta yadda al'ummomin kasa da kasa za su samu zarafin fuskantar kalubalolin da abin ya shafa cikin hadin gwiwa. (Maryam)