in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sami ci gaba sosai a fannin kiyaye nau'oin halittu
2015-12-04 10:52:52 cri
Bisa alkaluman da hukumar kiyaye muhalli ta Sin ta fitar a kwanan baya, an ce Sin tana da dukkan tsare tsaren kare halittu, kuma yawan tsirrai a kasar bisa jimilla ya kai sama da dubu 35, adadin da ya kai matsayi na uku a duniya, don haka kasar ta Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi samun nau'oin halittu daban daban.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, Sin tana da nau'oin dabbobi masu kashin baya sama da dubu 8, yayin da ta yi rajistar nau'oin halittun teku sama da dubu 28, adadin da ya shaida yawan albarkatun halittu masu dimbin yawa da kasar ke da su.

Bayan haka, Sin wuri ne da aka fara shuka shinkafa da wake da sauransu a duniya, inda yawan tsirrai da aka shuka, da yawan dabbobin da ake kiwo a gida, suka kai matsayi na farko a duniya baki daya. Bisa kokarin daukacin al'ummar ta, an kusan kammala aikin kafa tsarin kiyaye ire iren halittu a Sin.

Bugu da kari, Sin tana dora muhimmanci sosai kan ba da kariya ga nau'oin halittun, wanda hakan ya sa ta zama daya daga cikin kasashen da suka daddale yarjejeniyar kiyaye nau'oin halittu ta MDD karo na farko. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China