Shugaba Zuma ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a birnin Pretoria, inda ya yi fatan yarjejeniyar za ta taimaka wajen samar da makoma mai kyau ta hanyar magance matsalar sauyin yanayi baki dayan ta.
Zuma ya ce, baki dayan kan kungiyar G77 da kasar Sin wadda kasar ta Afirta ta kudu ke jagoranta a hade yake a taron na Paris, inda suka gabatar da bukatunsu da suke fatan ganin an amince da shi cikin murya guda.
A ranar Asabar ne aka kai ga cimma yarjejeniya ta karshe a taron sauyin yanayi na duniya da MDD ta shirya a birnin Paris na kasar Faransa, inda ake fatan kasashen duniya za su rage yawan iskar da ke dumama yanayin duniya da suke fitarwa nan da shekara 2020.(Ibrahim)