Ma Xiaoguang ya bayyana cewa, a watan Faburairu na shekarar 2014, shugaban ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na Sin da shugaban kwamitin MAC sun gana da juna a birnin Nanjing, inda suka dora niyyar kafa tsarin mu'amala tsakaninsu a kullum bisa matsaya daya da aka cimma a shekarar 1992. A cikin shekaru biyu da suka wuce, ofishin da kwamitin sun yi mu'amala da juna cikin yakini, tare da daidaita matsaloli da dama yadda ya kamata, hakan ya sami amincewar bangarori daban daban na sassan biyu. Tsarin mu'amala da juna tsakanin ofishin da kwamitin ya taimaka wa bangarorin biyu wajen samun fahimtar juna da amincewa da juna, ta yadda za a cimma burin bunkasa dangantaka tsakanin mashigin tekun Taiwan.(Fatima)