Yayin taron manema labaru da ya gudana a yau din, Madam Hua ta jaddada cewa manufar kasar Sin daya tak ta samu amincewar kasa da kasa, ta kuma zama babban tushen siyasa, a fannin raya dangantaka tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. Don haka a koda yaushe gwamnatin Sin ba za ta canza matsayin ta na siyasa game da manufar kasar Sin daya tak a duniya ba. Za kuma ta yaki dukkanin masu fatan ballewar yankin Taiwan daga babban kasar Sin, da masu fatan kafa kasar Sin guda biyu, da ma wadanda ke da burin ganin an kafa kasar Sin da kasar Taiwan tare.(Fatima)