Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Juma'ar nan, ta yi kashedin cewa, duk wani yunkuri na neman 'yancin yankin Taiwan, na iya haifar da kazamin tashin hankali a mashigin yankin baki daya.
Sanarwar dai na zuwa ne bayan kalaman da sabuwar shugabar yankin na Taiwan Tsai Ing-wen ta gabatar yayin rantsuwar ta ta kama aiki, wadanda a cewar sanarwar basu fayyace karara aniyar ta game da muhimman batutuwa masu alaka da mashigin Taiwan din ba.
Cikin jawabin shugabar ta Taiwan, akwai kalamai masu harshen damo, wadanda suka bar jama'a cikin duhu game da alakar babban yankin kasar Sin da yankin na Taiwan, ba kuma ta tabo batun yarjejeniyar shekarar 1992, da ma tasirin ta ga zaman lafiyar sassan da ta shafa ba.
Kaza lika sanarwar ta ce shugaba Tsai, ba ta fayyace dabarun da ya dace a bi wajen wanzar da zaman lafiya, da daidaito da ci gaba tsakanin sassan game da mashigin Taiwan din ba.(Saminu)