Wakilin kasar Sin dake hukumar FAO Niu Dun da babban sakataren hukumar Jose Graziano da Silva sun yanke kyallen dake nuna alamar bude taron, sa'an nan suka gabatar da jawabai.
A jawabinsa yayin bikin, Niu Dun ya ce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali matuka kan ayyukan kawar da talauci, tana kuma zuba jari masu dimbin yawa kan ayyukan da abin ya shafa a ko wace shekara domin taimakawa masu fama da talauci na kasar wajen fitar da su daga kangin talauci da kuma samun wadata.
Haka kuma, gwamnatin kasar Sin tana ci gaba da karfafa ayyukan gina ababen more rayuwa da kayayyakin tallafawa al'ummomin da ke yankunan karkarar kasar, ta yadda za a kyautata ayyukan yawon shakatawa a yankin, baya ga samar da horo kan ayyukan yawon shakatawa ta yadda al'ummomin da ke karkara za su raya wannan aiki. Hasashe na nuna cewa, ya zuwa shekarar 2020, Sinawa kimanin miliyan 12 za su iya fita daga kangin talauci ta hanyar bunkasa aikin yawon shakatawa.
A nasa jawabin, Jose Graziano da Silva ya ce, kasar Sin tana ci gaba da ba da muhimmanci wajen raya kasa da kasa, ta kuma nuna wasu fasahohinta masu kyau kan aikin kawar da talauci a wannan taro na nuna hotuna.
Taken taron nuna hotunan da aka yi a birnin Roma shi ne "kawar da talauci ta hanyar raya aikin yawon shakatawa", inda aka nuna hotuna kan yadda ake raya aikin yawon shakatawa domin kawar da talauci, da kuma hotuna na kyakkyawar kasa ta Sin a yayin taron, da kuma wasu fasahohin kasar Sin wajen kawar da talauci ta hanyar bunkasa aikin yawon shakatawa, da sakamakon da aka cimma a kasar cikin 'yan shekarun da suka gabata, haka kuma, an nuna wasu kyawawan hotuna na wuraren shakatawar kasar Sin. (Maryam)