Su Guoxia ta kara da cewa, yawan matalauta a kasar Sin a shekarar 2015 ya ragu da miliyan 14 da dubu 420 bisa na shekarar 2014, kana yawan mutane da mai yiwuwa za su kasance cikin kangin talauci a kasar ya ragu daga kashi 7.2 cikin dari zuwa kashi 5.7 cikin dari. Kaza lika saurin ayyukan yaki da talauci ya karu bisa na shekarar 2014.
Hukumomi daban daban da abin ya shafa sun gabatar da matakan taimakawa yankuna masu fama da talauci. Kana bangarori daban daban sun tattara kudi da yawansa ya kai yuan biliyan 10 don yaki da talauci, kudaden da yawansu ya karu da ninka biyu bisa na shekarar 2014.
A shekarar 2015, an kara samar da kudi na musamman don yaki da talauci, ciki har da kudin da gwamnatocin lardunan kasar suka samar wato Yuan biliyan 33.5, wanda ya karu da kashi 25 cikin dari bisa na shekarar 2014. (Zainab)