Rahotanni na cewa, an bude wannan shafin Internet ne, don bullo da wani dandalin more fasahohi ko matakan da aka gano game da rage talauci, ta yadda za a inganta hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa a wannan fanni. An bude wannan shafi ne da harshen Turanci, kuma yana kunshe da bayanai game da nasarorin da Sin ta samu cikin shekaru 30 bayan da ta gudanar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, akwai kuma bayanai game da yadda kasar Sin ta rage talauci a kasar, inda aka yi bayani dalla-dalla ga gwamnatoci da hukumomin nazari kan batun rage talauci. Wasu hukumomin nazarin fasahar rage talauci na kasashen Asiya da Afrika da nahiyar kudancin Amurka su ma sun shiga cikin wannan dandali.
Mataimakin direktan sashen kula da rage talauci na majalisar gudanarwar Sin Hong Tianyun ya bayyana a yayin bikin cewa, yana fatan za a yi amfani da wannan shafin Internet, don kara tattauna dabaru da manufofin da za a yi amfani da su wajen rage talauci da samun bunkasuwa, ta yadda za a kirkiro wani sabon tsari da sabuwar manufa game da rage talauci a kasar Sin.(Bako)