Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya ce sassa daban daban za su yi hadin gwiwa don tabbatar da nasarar wannan kuduri. A cewar sa hakan bangare ne na aiwatar da manufofin ci gaban kasar Sin, tsakanin shekarar 2014 zuwa 2020, wanda ya tanaji fidda a kalla mutane miliyan 10 daga kangin fatara a duk shekara.
Liu ya yi hasashen cimma nasarar da aka sanya gaba a bana, duba da yadda aka samar da isassun kudaden taimakawa masu karamin karfi a fadin kasar.
Jami'in ya kara da cewa, tuni Sin ta cimma nasarar fidda al'ummun ta mazauna karkara kusan miliyan 100 daga halin matsi, daga shekarar 2010 ya zuwa yanzu, yayin da kuma ake ci gaba da kokarin tallafawa karin wasu mutanen miliyan 60 nan da karshen shekarar 2020. (Saminu Alhassan)