Garin Jinzhai yana yankin Dabie mai cike da tsaunuka, wannan ya sa ake kira sa da sunan wurin da aka kirkiro sojojin Red Army da hafsoshin soja, kana shi ne gari mafi fama da talauci a kasar Sin, ya zuwa karshen shekarar 2015, akwai matalauta fiye da dubu 80 a garin.
A wannan rana da yamma, shugaba Xi Jinping ya kai ziyara kauyen Dawan dake garin Jinzhai. Xi Jinping ya bayyana cewa, ba za a manta duk wani yanki ba yayin da ake kokarin cimma burin zaman wadata, musamman tsohon yankin kasar.
A lokacin yaki da 'yantar da jama'a ko a lokacin bude kofa da yin kwaskwarima, jama'ar yankin sun bayar da gudummawa sosai ga kasar. Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya dora muhimmanci sosai kan aikin yaki da talauci a yankuna masu fama da talauci, don haka kamata ya yi a dauki matakai tare da bullo da tsarin yaki da talauci na dogon loakci don aiwatar da aikin a dogon lokaci da tabbatar da cimma burin zaman wadata a dukkan fannoni kafin shekarar 2020. (Zainab)