A yayin taron, da farko, a madadin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, Xie Xiaoyan ya bayyana wasu abubuwa guda hudu da ake fatan cimmawa a taron na wannan karo. Na farko ya ce, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su aiwatar da kuduri mai lamba 2254 da kwamitin sulhu ya tsara kan batun Syria bisa dukkan fannoni, na biyu, ya kamata kasashen Amurka da Rasha su hada kai da mambobin kasashen kwamitin sulhu na MDD domin ba da karin gudummawa don ganin an tsagaita bude wuta a duk fadin kasar Syria, da kuma ciyar da yunkurin warware matsalar Syria ta hanyar siyasa gaba. Na uku shi ne, kasar Sin na fatan kasashe daban daban a yankin su dauki nauyin da ke kansu domin nuna goyon baya ga kasar Syria ta hanyoyin da za su dace a warware matsalar kasar ta hanyar siyasa. A karshe kuma, ana fatan bangarorin biyu na kasar Syria za su gaggauta yin shawarwari kai tsaye a tsakaninsu, domin lalubo hanyoyin warware matsalar kasar cikin sauri, ta yadda zai dace da moriyar kasar da kuma al'ummominta.
Kaza lika, Xie Xiaoyan ya ce, kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa, za su ci gaba da nuna goyon baya kan aikin da manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria Staffan de Mistura ya yi wajen warware matsalar Syria, haka kuma, tana kira ga mambobin tawagar kasa da kasa da ke goyon bayan Syria da su ba da karin taimako wajen aiwatar da yarjejeniyar dakatar da yake-yake, yaki da 'yan ta'adda dake kasar Syria, ciyar da yunkurin siyasa gaba da kuma kyautata yanayin jin kai na kasar, ta yadda za a samu ci gaba kan warware matsalar Syria.
A yayin taron ministocin na birnin Vienna, mahalata taron sun tattauna kan batutuwa da dama dake shafar tsagaita bude wuta a Syria, yanayin jin kai na kasar, da kuma yunkurin siyasar kasar da dai sauransu, daga karshe kuma, suka fidda sanarwar taron. (Maryam)