Rundunar sojan kasar Syria ta ce, dakarun 'yan adawa sun kai hari a yankin dake karkashin ikon sojojin gwamnatin kasar ne, 'yan mintoci da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta na gajeren lokaci da aka cimma. A daya hannun kuma, reshen kungiyar al-Qaeda dake kasar Syria wato kungiyar Jabhatal-Nusra ya kai hari yankin dake karkashin ikon sojojin gwamnatin kasar dake birnin Aleppo. Sai dai kuma, rundunar sojojin gwamnatin kasar ta mai da martani ga hare-haren da suka kai mata.
A halin yanzu dai, bangaren adawar bai fidda wata sanarwa game da wannan batu ba.
a baya, Birnin Aleppo ya kasance cibiyar tattalin arziki, kuma birni mafi girma na kasar Syria, sai dai yanzu birnin yana karkashin ikon sojojin gwamnatin kasar, dakarun adawa da kuma kungiyar masu tsattsauren ra'ayin kasar. (Maryam)