in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya dace bangarorin Syria su saka bukatar jama'ar kasarsu sama da komai, in ji wakilin Sin
2016-05-05 10:17:24 cri
Zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a yayin taron tattaunawa game da batun Syria da kwamitin sulhu na MDD ya kira a ranar 4 ga wata cewa, a halin yanzu, ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a wasu yankunan kasar Syria, musamman ma a birnin Aleppo, don gane da wannan lamari ya ce, ya kamata bangarorin daban daban da abin ya shafa su mai da moriyar kasa da ta al'ummomin kasar a gaban komai, sannan a cigaba da nanata batun tsagaita bude wuta a kasar yadda ya kamata, bisa kudurorin da abin ya shafa da kwamitin sulhu na MDD ya tsara, yayin aiwatar da yarjejeniyar tsayar da rikice-rikice a kasar, sa'an nan a dakatar da hare-haren da za a kai ga fararen hula da kayayyakin jin kai, domin shimfida zaman lafiya a kasar cikin sauri.

Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da samar da taimako yadda ya kamata domin ciyar da aikin warware matsalar Syria gaba bisa ka'idar adalci da kuma bisa dukkan fannoni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China