in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An halaka wani babban kwamandan Hezbullah a Syria
2016-05-13 20:19:35 cri

A yau Jumma'a ne kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon ta sanar da mutuwar babban kwamandanta, Mustafa Badr Al-Din sanadiyar wani harin da aka kai a kasar Sham. Amma kungiyar tana bin bahasin lamarin.

Wata sanarwar da kungiyar ta bayar ta ce, tana kokarin tabbatar da wannan lamari da kuma dalilin aukuwarsa, tare da gano ko an kai harin ne ta sama, ko roka ne ko kuma bam din da aka yi amfani da shi wajen kai harin. Ko da yake kungiyar ba ta yi wani karin haske ba, ko kuma lokacin da aka kai shi wannan harin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China