A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taron gaggawa kan yanayin da birnin Aleppo ke ciki a halin yanzu, inda Mr. Feltman ya ce, ya kamata a warware rikicin Syria ta hanyar siyasa, haka kuma, MDD na son ba da taimako yadda ya kamata domin farfado da shawarwarin neman sulhu a Syria cikin hanzari.
A nasa bangaren, mataimakin babban magatakardan MDD mai kula da harkokin jin kai Stephen O'Brien ya bayyana a yayin taron cewa, al'ummomin dake birnin Aleppo suna ci gaba da fuskantar tabarbarewar yanayin zaman rayuwarsu, shi ya sa, yake sa kaimi ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su bi dokokin kasa da kasa yadda ya kamata, da kuma ba da taimako gare su ta hanyoyin da suka dace. (Maryam)