An kai harin ne a wata tashar bincike ta rundunar sojan kiyaye jama'ar kurdawa dake birnin Kameshli. Kamfanin dillancin labaru na Syria ya ba da labari dangane da haka, amma kawo yanzu ba a san kowane ne ya kai wannan hari ba.
Yawan kurdawa ya kai kashi daya bisa goma na yawan mutanen Syria, yawancinsu suna zama a yankin iyakar kasa tsakanin arewacin Syria da Iraki da kuma Tukiyya, kuma birnin Kameshli da aka kai hari a wannan karo matsugunin kurdawa ne.
A wannan rana kuma, an kai harin boma bomai da aka dasa cikin mota a jihar Deir ez-Zor dake gabashin kasar, amma ya zuwa yanzu babu wata masaniya kan yawan mutanen da suka mutu ko jikkata ba.(Fatima)