in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha da Amurka za su dauki matakan tabbatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Syria
2016-05-10 11:27:49 cri

A jiya Litinin, kasashen Rasha da Amurka sun ba da sanarwa ta hadin gwiwa game da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Syria, da bada tallafin jin kai, da kuma daidaita batun Syria ta hanyar siyasa, inda bangarorin biyu suka tabbatar da cewa, za su dauki matakai domin tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a duk fadin kasar ta Syria.

Bisa ga sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayar a jiya Litinin, an ce, kasashen Rasha da Amurka sun sake nanata alkawarinsu na tsagaita bude wuta a Syria, kuma sun gabatar da matakai guda biyar domin tabbatar da wannan yarjejeniya, wadanda suka hada da ingiza bangarori daban daban da su gudanar da yarjejeniyar, da dakatar da kai farmaki ga fararen hula, da manyan ayyukan yau da kullum da kuma ayyukan jinya, da hana kai farmakin ta sama a matsugunai da kuma kungiyoyin dake bin yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da yin kira ga kasashen duniya da su daina tallafawa kungiyar IS da kuma sauran kungiyoyin ta'addanci, da hana 'yan ta'adda tsallakawa iyakar kasar Syria.

Kasashen Rasha da Amurka, za su dauki matakai kan wuraren dake karkashin ikon kungiyoyin 'yan ta'adda.

A wannan rana kuma, ministan harkokin wajen Rsaha Sergei Lavrov, da takwaransa na kasar Amurka John Kerry sun yi musayar ra'ayi ta wayar salula, inda suka cimma matsaya daya cewa, hadin gwiwar kasashen biyu a fannin ayyukan soja na da muhimmanci sosai ga kasar Syria.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China