in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa za ta fara gudanar da bincike kan Isra'ila
2015-01-17 17:18:42 cri
Babbar kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta ICC mai hedkwata a birnin Hague, ta fidda wata sanarwa dake nuna cewa, bisa bukatun da Falesdinu ta gabatar mata, za ta fara gudanar da bincike kan zargin da ake yiwa kasar Isra'ila na aikata laifuffukan yaki.

Falesdinu dai ta bukaci kotun ta ICC da ta fara gudanar da bincike game da wannan zargi a matakin farko, game da laififfukan da Isra'ilan ta aikata a yankunan Falesdinu da Isra'ilan ta mamaye yayin dauki ba dadin da ya wakana tsakanin bangarorin biyu cikin watan Yunin bara.

Babu dai wata doka da ta kayyade tsawon lokaci da za a shafe ana gudanar da irin wannan bincike a matakin farko, cikin yarjejeniyar birnin Rome wadda ta tanaji hukunta manyan laifuffukan kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China