Darektan cibiyar lafiya ta al'ummar palasdinawa da ke Ramallah Ahmed Bitawi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa,matashin mai suna Wisam Farraj dan shekaru 20 da haihuwa ya mutu ne sakamakon harbin da 'yan sandan Isra'ila suka yi masa a kirji.
Rahotanni na cewa, an kwashe kusan mako guda ana tashin hankali a yammacin gabar kogin Jordan da gabashin birnin Kudus, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Palasdinawa 7 da Yahudawan Isra'ila 4.
Majiyoyin asibiti na Palasdinawa sun bayyana cewa, daruruwan Palasdinawa ne suka yi taho mu gama da jami'an tsaro, inda suka ke jifan su da duwatsu da bama-baban wuta inda 'yan sanda 9 suka jikkata, baya ga wasu magidanta da dama da suma suka jikkata sanadiyar arangamar.
Bugu da kari, hukumar Palasdinawa ta yi allah-wadai da harin da Yahudawan Isra'ila su ka kaiwa ministanta na sadarwa Allam Musa a kan hanyarsa ta zuwa birnin Nablus da ke kusa da gabar yammacin kogin Jordan
Har yanzu dai gwamnatin Isra'ila ba ta ce komai ba game da wannan lamari.(Ibrahim)