in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minsitan harkokin wajen Sin ya kai ziyarar aiki a Tunisiya
2016-05-14 13:27:53 cri
Jiya Asabar 13 ga wata, bi da bi shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi da firaministan kasar Habib Essid suka gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi wanda ya kai ziyarar aiki a kasar Tunisiya.

A yayin ganawar tasu, shugaba Essebsi ya ce, yana maraba da zuwan karin kamfanonin kasar Sin a kasar Tunisiya domin taimakawa kasar samar da ababen more rayuwa.

Sa'an nan kuma, firaminista Essid ya bayyana cewa, ana fatan kasar Sin za ta iya nuna goyon baya da kuma ba da taimako ga kasar Tunisiya a fannonin fuskantar kalubalolin da suke shafi tsaro, zamantakewar al'umma da kuma tattalin arziki, haka kuma, kasar Tunisiya tana son karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin ciniki, zuba jari, yawon shakatawa, gina ababen more rayuwa da dai sauransu.

A nasa bangaren kuma, Wang Yi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Tunisiya wajen neman hanyar raya kasa ta musamman dake dacewa da yanayin kasa da kuma moriyar al'ummomin kasar, haka kuma, kasar Sin tana son sa kaimi ga kamfanonin kasar da su yi hadin gwiwa da zuba jari kan manyan ayyukan gina ababen more rayuwa a kasar Tunisiya, shi ya sa, ana fatan kasar Tunisiya za ta iya samar da yanayin tsaro da zuba jari mai kyau ga kamfanonin kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China