in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandanTunisiya sun cafke masu tsattsauran ra'ayi 16
2016-05-12 11:14:26 cri
A jiya Laraba 11 ga wata, ma'aikatar harkokin cikin gida ta Tunisiya ta ba da sanarwar cewa, a wannan rana, 'yan sanda sun hallaka wasu mutane 2, tare da cafke wasu mutanen16 da ake tuhuma da laifin a yayin da suke farautar wasu masu tsattsauran ra'ayi a Tunis, hedkwarar kasar, .

Sanarwar ta ce, bisa bayanan sirri da bangaren 'yan sanda ya samu, an ce, wasu gungun dakarun dauke da makamai sun buya a lardin Ariana dake arewa da birnin Tunis wato hedkwatar kasar. Don haka, 'yan sandan sun kai samame wurin, inda suka yi musayar wuta da dakarun tare kuma da kwace makamai da dama.

Bisa labarin da kafofin yada labarum kasar suka bayar, an ce, a cikin wadannan dakaru, akwai wadanda ake tuhumarsu da hannu a harin da aka kai a birnin Ben Guerdane dake yankin kudu maso gabashin kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China