in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a cimma wata yarjejeniyar sasanta 'yan Libiya nan bada jimawa ba a Tunis, a cewar kafofin watsa labaran Tunisiya
2015-12-07 10:46:01 cri
A yayin wani taro a yammacin ranar Asabar zuwa Lahadi a wata unguwar birnin Tunis, wanda ya gudana tsakanin wakilan majalisar dokokin kasar Libiya da majailsar dokokin Tobrouk, an bayyana cewa akwai yiyuwar a cimma wani sulhu domin warware rikicin Libiya, a cewar kafofin watsa labaran kasar Tunisiya a rana Lahadi. A cewar kafar Al-Arabia, wannan ita ce yarjejeniyar da ta shafi neman sasantawa ta fuskar siyasa tsakanin bangarorin kasar Libiya masu gaba da juna. Daga cikin batutuwan da wannan yarjejeniya ta tanada akwai batun kafa gwamnatin hadaka a cikin wa'adin kwanaki 25 da kuma maido da kundin tsarin mulki na shekarar 1963 bayan an yi masa wasu gyare gyare. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China