Ministan harkokin wajen Tunis Khemaies Jhinaoui ya shedawa 'yan jaridu bayan wata ganawa da takwaransa na kasar Algeriya Ramtane Lamamra , inda ya bukaci bangarorin da basa ga maciji da juna a Libyan dasu zauna a teburin sulhu da bangaren gwamnatin kasar domin warware takaddamar dake tsakaninsu don kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Bugu da kari, babban jami'in diplomasiyya na kasar Algeriyar ya bayyana cewar, kasarsa ta yi amanna cewar amfani da karfin soji ba zai taba yin tasiri ba wajen kawo karshen rikicin kasar ta Libya.
Ya ce suna fatar kasancewa makwabta masu taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin kasar Libya amma ba masu haddasa matsala ba.
Ya kara da cewar, a kwanan nan wasu kasashen yammacin duniya sun sha yunkurin amfani da karfin tuwo wajen fatattakar mayakan kungiya mai fafutukar kafa daular musulunci wato IS daga kasar.
Kasar Libya ta tsunduma cikin rudani ne tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011.(Ahmad Fagam)