in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaron kasar Tunisiya ta hallaka dakaru 28
2016-03-08 10:52:27 cri

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Tunisiya ta tabbatar a jiya Litinin cewa, rundunar tsaron kasar ta hallaka dakaru 28 a wannan rana a birnin Ben Guerdane dake kudu maso gabashin kasar.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Tunisiya ya bayyana cewa, wasu dakaru sun kai farmaki ga wani sansanin soja na birnin Ben Guerdane da safiyar wannan rana, rundunar tsaron ta hallaka dakaru 28 a yayin musayar wuta, kana an kama wasu dakarun 7, amma wasu fararen hula 7 sun mutu a sakamakon lamarin. Ban da haka kuma, sojoji 10 sun mutu. A halin yanzu, rundunar tsaron kasar ta daidaita al'amurra game da halin da ake ciki a wurin, kana suna kokarin kama sauran dakarun da suka tsere.

A sa'i daya kuma, firaministan kasar Tunisiya Habib Essid ya kira taron gaggawa, kana ya tura ministocin harkokin cikin gida da tsaro zuwa birnin Ben Guerdane domin karfafa tsaron birnin. Bugu da kari, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Tunisiya ta sanar da kafa dokar takaita zirga zirga daga karfe 7 na dare zuwa karfe 5 na safe na yau.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China