in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar garda sarki a Tunisiya ta dakile wani harin ta'addanci a iyakar kudu maso yammacin kasar da Aljeriya
2016-01-26 11:18:54 cri

A daren Lahadi zuwa Litinin da suka gabata, wasu rukunonin jami'an tsaro na garda sarki na kasar Tunisiya sun dakile wani harin ta'addancin da ya doshi wata tashar tsaro da ke kan iyakar dake Om-Larayes, wani yankin Gafsa dake kudu maso yammacin kasar, in ji kakakin garda sarkin Khalifa Chaabani.

Bisa tsawon kimanin mita 300 da iyaka da kasar Aljeriya, wannan tashar tsaro ta fuskanci wani harin daga wani gungun 'yan ta'adda dauke da mamakai wadanda suka fito daga kasar Aljeriya, a cewar kanal Chaabani.

Kakakin ya kara da cewa, da farko 'yan ta'addan sun yi kokarin farma wani rukunin garda sarki dake sintiri a lokacin da yake kan hanyarsa dawo tashar.

An yi musanyar wuta mai karfi tsakanin maharan da masu garda sarkin, da suka dauki na wani rukunin soja kafin wadannan 'yan ta'adda su ja baya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China