in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan Syria ya sanar da tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta
2016-05-02 12:11:18 cri
A jiya Lahadi ne rundunar sojan kasar Syria ya sanar da cewa, za a tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Damascus fadar mulkin kasar, da kuma East Gouta dake gabashin karkarar birnin.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya ruwaito wata sanarwar daga rundunar wadda ke cewa za a tsawaita wa'adin ne da kwana guda, domin hana kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, da dakaru masu adawa da gwamnati samun duk wata dama ta kaddamar da hare hare kan fararen hula.

Sai dai a daya bangaren dakaru masu adawa da gwamnatin kasar sun yi watsi da wannan kuduri na tsagin sojojin gwamnati na tsagaita bude wuta. Kaza lika ita ma kungiyar Free Syrian Army ta fidda wata sanarwa, inda ta nuna adawar ta da tsagaita bude wuta a wadannan yankuna.

A ranar 22 ga watan Fabarairu ne kasashen Amurka da Rasha, suka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin bangarori daban daban da rikicin kasar Syria ya shafa, kana an soma gudanar da yarjejeniyar tun daga ranar 27 ga watan na Fabarairu.

A baya bayan nan an kaddamar da farmaki sau da dama a wasu yankunan kasar ta Syria, ciki kuwa hadda hari mafi tsanani a birnin Aleppo dake arewacin kasar. Wannan mataki da ya zama tamkar gurgunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kasashen Amurka da Rasha da suka cimma, ya kasance dalili, da ya sanya rundunar sojan Syriar sanar da tsagaita bude wuta a wasu yankuna dake kewaye da birnin Damascus, da East Gouta da kuma Lattakia. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China