in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga bangarori daban daban na Syria da su amince da tsagaita bude wuta
2016-05-03 20:09:03 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya bayyana cewa Sin na maida hakali ga yanayin tsanantar rikice-rikice a wasu yankunan kasar Syria, wadanda ke haddasa rasa rayuka da jikkatar mutane masu yawa. Kaza lika Sin na kira ga bangarori daban daban da rikicin Syria ya shafa, da su rungumi batun tsagaita bude wuta.

Har wa yau Hong Lei ya jaddada cewa, Sin na goyon bayan bangarori daban daban da rikicin kasar ya shafa, game da kudurin kara fadada hadin gwiwa, tare da tsara shirin warware rikicin kasar ta Syria. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China