A yayin ganawarsu, minista Ghandour ya nuna godiya ga kasar Sin wajen ba da gudummawa ga cimma nasarar dandalin tattaunawar, ya yi imani da cewa, dandalin zai sa kaimi ga dangantaka tsakanin kasashen Larabawa da Sin zuwa wani sabon mataki. Ya kara da cewa, Sudan tana nuna goyon baya ga matsayin da Sin ke dauka kan batun tekun kudancinta, tana nuna goyon baya ga kokarin da Sin ke yi na kiyaye cikakken yankin kasa da iko da moriyarta bisa dokoki. Dadin dadawa, minista Ghandour ya gabatar da yanayin da ake ciki a Sudan da kuma yunkurin tabbatar da zaman lafiya a kasar, ya ce, Sudan tana godiya ga kasar Sin wajen nuna goyon baya ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya a kasar da taimakawa bunkasa tattalin arzikinta. Da fatan Sin za ta ci gaba da nuna mata goyon baya kamar yadda ta saba.
A nasa bangare, minista Wang Yi ya bayyana cewa, Sin za ta tsaya tsayin daka kan nuna goyon baya ga kasar Sudan wajen samun moriyarta bisa dokoki kan batun Darfur da sauransu, kuma za ta ci gaba da sa kaimi ga kamfanonin Sin da su gudanar da harkokinsu a Sudan. Da fatan Sudan za ta yi amfani da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa, domin karfafa hadin gwiwarta da Sin yadda ya kamata.(Fatima)