in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da muhimmin ci gaba da aka samu a yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu
2016-04-27 19:48:15 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru a yau Laraba cewa, kasar Sin ta yi maraba da muhimmin ci gaba da aka samu a yunkurin da ake yi na shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu.

A jiya Talata, shugaban 'yan adawa na kasar Sudan ta kudu Riek Machar ya koma birnin Juba, babban birnin kasar, inda ya yi rantsuwar kama aikin a matsayin mataimakin shugaban kasar.

Madam Hua Chunying ta bayyana a yayin da take amsa tambayoyin manema labaru cewa, wannan wani muhimmin ci gaba ne da aka samu a kokarin da ake yi na shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu, kuma kasar Sin ta yi maraba da wannan ci gaba sosai.

Bugu da kari, Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar kawar hadin gwiwa ce ta kasar Sudan ta kudu. Tun bayan da rikici ya barke a kasar Sudan ta kudu a shekarar 2013, kasar Sin ta rika shiga aikin shimfida zaman lafiya a kasar, ta kuma amsa bukatun kasashen Afrika wajen daidaita batutuwan da suka shafe su ta hanyar da suke so, ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen ingiza bangarori daban daban na kasar Sudan ta kudu da su kulla yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a tsakaninsu.

Ban da haka kuma, Hua Chunying ta ce, kasar Sin tana fatan bangarori daban daban na kasar Sudan ta kudu za su ci gaba da yin kokari tare wajen kafa gwamnatin hadaka ta wucin gadi domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman bunkasuwa a kasar. Kasar Sin tana son ci gaba da taka rawa mai yakini a kan wannan aiki tare da sauran kasashen duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China