A yau Talata ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Sudan Omar al-Bashir a nan birnin Beijing.
A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi wa al-Bashir maraba da zuwa nan kasar Sin, inda zai halarci bikin murnar cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da maharan Japan da ma yaki da masu ra'ayin nuna karfi a fadin duniya.
Shugaba Xi ya ce, sanarwar hadin gwiwa da Sin da Sudan za su daddale dangane da kafa huldar abokantaka tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, wani sabon babi ne a tarihin bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen 2.
Don haka wajibi ne kasashen 2 su kara amincewa da juna ta fuskar manyan tsare-tsare, kana su ci gaba da mara wa juna baya a muhimman al'amuran da ke jawo hankalinsu. Kasar Sin na son ci gaba da bai wa Sudan goyon baya ta fuskar basirar raya tattalin arziki da zaman al'ummarta.
A nasa bangaren, shugaba al-Bashir ya ce, yana matukar farin cikin halartar bikin murnar cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da maharan Japan da ma yaki da masu nuna ra'ayin karfi a duniya tare da Sinawa. kasarsa tana fatan habaka hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2.
Bugu da kari, Sudan ta yaba da shirin nan na "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, kuma tana son shiga a dama da ita wannan shiri.
A wannan rana kuma, Zhang Gaoli, mataimakin firaministan kasar Sin shi ma ya gana da shugaba al-Bashir. (Tasallah Yuan)