in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakaru masu adawa na kasar Sudan ta Kudu sun yi barazanar kai hari ga mahakar mai
2015-05-22 17:59:38 cri

Rikice-rikice sun kara tsananta a jihar Upper Nile da sauran wurare a kasar Sudan ta Kudu, har ma dakaru masu adawa na kasar sun yi barazanar kai hari ga mahakar mai da sauran wuraren ayyukan more rayuwa.

A game da hakan , Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru a yau Juma'a 22 ga wata cewa, Sin ta damy matuka a kan wannan al'amari.

Hakazalika kuma, Hong Lei ya jaddada cewa, kasar Sin ta taba bayyana sau da dama cewa, babu yiwuwa ne a warware rikicin kasar Sudan ta Kudu ta hanyar nuna karfin tuwo ba. Kasar Sin ta kalubalanci bangarori daban daban da rikicin ya shafa da su tsaida kuduri da cimma daidaito da samun sulhu cikin hanzari da kuma bude yunkurin samar da wani yanayi na wucin gadi a kasar. A halin yanzu, kasar Sudan ta Kudu tana fuskantar kalubale a fannonin moriyar jama'ar kasar da zaman lafiyar kasar. Kasar Sin ta yi kira ga bangarori biyu da rikicin ya shafa da su yi la'akari da makomar jama'ar kasar Sudan ta Kudu tare da dakatar da rikice-rikice ba tare da bata lokaci ba, sa'an nan su tabbatar da tsaron ma'aikatan kasashen waje da ma'aikatan MDD da hukumomin samar da gudummawar jin kai dake kasar Sudan ta Kudu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China