in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga jaridun Najeriya
2016-05-12 19:23:29 cri

A jiya Laraba ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarci manyan dillalan mai a kasar da su rika sayar da man fetur akan naira 135 zuwa 145 kan kowa ce lita. Bayan da gwamnatin ta baiwa 'yan kasuwa iznin shigo da man.kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa

Ita kuma jaridar Guradian ta ruwaito shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yana cewa, ba zai nemi gafara daga firaministan Burtaniya David Caneron kan kamalan da ya yi ba cewa, kasashen Najeriya da Afghanistan sune kan gaba wajen cin hanci. Maimakon haka ya taimaka wajen ganin an maido mata da kadarorin da aka sata wadanda yanzu haka suke cikin kasar.

Daga karshe jardar Daliy Trust ta ba da labarin cewa, kungiyar kare hakkin bil-adama ta kasa da kasa ta bayyana cewa, a kalla mutane 149 ciki har da kananan yara 'yan kasa da shekaru 6 ne suka mutu a watan Fabrairun wannan shekara, baya ga wasu mutane sama da 1,200 da har yanzu suke tsare a barikin Giwa da ke jihar Borno.

Sai dai kuma mai magana da rundunar sojojin kasar Kanar Sani Usman ya karyata wannan zargi na kungiyar Amnesty.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China