in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga jaridun Najeriya
2016-05-11 19:17:43 cri

Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin samar da burtalolin shanu a sassa daban-daban na kasar, a wani mataki na kawo karshen rikicin manoma da Fulani makiyaya da ke faruwa a kasar, kamar yadda jaridar Guardian ta wallafa.

A labarin da ta wallafa, jaridar Punch ta labarta cewa,a jiya Talata an sake samun bullar dogayen layukan ababan hawa a gidajen mai a jihohin Lagos da Ogun, kwanaki kadan bayan lafawar karancin man. Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da jita-jitar da ake yayatawa cewa, za a kara farashin man, lamarin da ya sa jama'a ke kokarin ganin sun sayi man kafin karin farashin ya fara aiki.

Ita kuma jaridar Daliy Trust ta ba da labarin cewa, wasu da ake zaton 'yan kungiyar asiri ce sun kashe mutane biyar a sassa daban-daban na jihar Rivers,baya ga harin da aka kaiwa harabar babbar kotun jiha da ke garin Fatakwal.

Hedkwatar tsaron Najeriya(DHQ) ta bayyana cewa, sojoji za su dauki dukkan matakan da suka dace bisa doka, don ganin sun murkushe duk wani mutum ko kungiya da ta yi kokarin lalata kayayyakin gwamnati.

Wata sanarwa da kakakin hukumar Birgediya janar Rabe Abubakar ya rabawa manema labarai ta bayyana cewa, hedkwatar tsaron kasar tana sane da bullar wata kungiya a yankin Niger Delta wadda ke kokarin kawo nakasu ga harkokin tattalin arzikin kasa ta hanyar lalata bututan mai, sace mai da kuma sace baki 'yan kasashen waje da ke aikin hako mai a yankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China