in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana shirin aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar jama'ar kasar
2016-05-05 09:17:38 cri

Karamar minista mai kula da kasafin kudi da tsare-tsare ta Najeriya Zainab Ahmed ta bayyana cewa, kasar tana shirin gudanar da wasu muhimman shirye-shirye 34 a wani bangare na matakan aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2016.

Ministar wadda ta shaida wa manema labarai hakan bayan kammala taron majalisar ministocin kasar karo na 67, ta ce, shirye-shiryen da ma'aikatar ta tsara, kana suka samu amincewar majalisar ministoci, za su taimaka wa gwamnati cimma manufofin da ta tsara cikin kasafin kudin kasar na shekarar 2016.

Ta kara da cewa, an kasa wadannan shirye-shirye 34 zuwa manyan manufofi 4, wadanda suka hada da manufofin tafiyar da mulki, harkar tsaro, fadada tattalin arziki, yadda za a tallafawa marasa karfi, da kuma yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar zuba jari da sauransu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China