in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta fara amfani da fasahar tantance mutane domin dakile fasa kwaurin makamai
2016-05-11 10:01:25 cri

Ministan harkokin cikin gidan Najeriya Abdurrahman Danbazzau ya ce, nan gaba kadan jami'an tsaron kasar za su fara amfani da hanyoyin tantance mutane na zamani, domin dakile laifuka masu alaka da fasa kwaurin makamai, da muyagun kwayoyi.

Danbazzau wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin taron jin ra'ayin jama'a wanda aka shirya a jihar Kaduna, domin bikin cikar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari shekara guda a kan mulki, ya ce, amfani da hanyoyin tantance jama'a ta amfani da hoton yatsun hannu, zai taimaka matuka, wajen kawo karshen fataucin muggan kayayyaki ta kan iyakokin kasar.

Ministan ya kuma kara da cewa, jami'an tsaro na aiki ba dare ba rana, don ganin sun magance aukuwar muggan laifuka a fadin kasar, ciki hadda garkuwa da mutane, da lalata bututun mai, da matsalar makiyaya dake aukawa al'umma, da kuma fashi da makami.

Ya ce, gidajen yarin Najeriya na fuskantar cunkoson firsinoni, matsalar da a yanzu haka gwamnatin kasar mai ci ke nazarin shawo kan ta, ciki kuwa hadda batun maida wasu daga gidajen yarin hannun sassa masu zaman kan su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China